Shin Abinda Tambuwal yayi Abin A Yabane ko A kasin Haka ? – Prof Umar Muhammad Laddo
Muna maraba da abinda Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi a wajen zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP inda ya janye takararsa don dan uwansa Atiku Abubakar ya ci zaben. Wannan shi ne a takaice muke kira da sunan Tambuwalci, ko kuma Tambuwaltaka, a siyasar Nijeriya. Muna fata wannan zai zama wani ginshiki na siyasarmu a nan gaba.
A fili take cewa idan da Tambuwal bai janye takararsa ba, da Gwamnan jihar Rivers ne, Nyesom Wike, zai cinye zaben na zama dan takarar jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa badi in Allah ya kai mu. Wannan hadiye kwadayi da Aminu Tambuwal ya yi yana nuna cewa shi ya nuna a siyasa, kuma yana sanya maslahar al’ummarsa a gaba da tasa maslahar ta kashin kansa.
Taron dangi don murkushe Gwamna Wike ya zama wajibi a wannan gaba ta siyasar kasarmu inda ya zama dole mu aje bambance-bambancenmu a gefe guda don tabbatar da maslaharmu a al’ummace. Kuma abin ya fi zama wajibi kasancewar shi Gwamnan na Rivers mai tsaurin ra’ayin Kiristanci ne wanda a wani lokaci ya yi shelar jiharsa a matsayin jihar Kirista bayan rushe wani masallacin Musulmi a babban birnin jihar tasa.
Yaudara da hila a siyasa, da ma nuna jan ido idan bukata ta kawo hakan, ba laifi ba ne ko kadan a takun siyasa, kuma babu abin kunya ko zargi a ciki, sai ma burgewa da cancantar yabo matukar dai manufar mai kyau ce, kamar yadda abin yake a nan.
Yana da kyau mu sani cewa rike mulki dun-dun-dun a Arewacin kasar nan kuma a hannun Musulmi dai-dai ne kuma ya dace da adalci. Da farko dai, wadanda suka fi yawa su ya dace da su yi mulki a ko yaushe. To mu ne muka fi yawa. Na biyu, abokan zamanmu sun kame wasu fagagen rayuwa a kasar nan wanda idan mu muka rike mulki zai zama an yi raba-dai-dai ke nan. Dalili na uku Allah ya yi mana baiwa da iya kwatanta adalci da kuma iya mulki duka a dalilin addininmu na Musulunci da kuma kayan gadonmu na tarihi. Wadan nan abubuwa duka sun saka mu a gaba idan ana zancen jahiranci da mulkin kasar nan.
A hakika tun tuni ya kamata a ce mun tabbatar da wannan amma hakan ba ta samu ba har zuwa yau. Amma muna fata a yanzu lokaci ya yi da za’a kafa wannan yanayi kuma a tabbatar da shi cewa, mulkin kasar nan ya zauna a Arewa dun-dun-dun. Babu wani abinda zai hana haka sai rashin karfin niyya da azama a bangaren shugabanninmu da jagororinmu.
Muna fata za mu ga Tambuwalci a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC wanda za a gudanar a kwana shida masu zuwa. A samu yan takara na manyan jam’yyu daga Arewa, kuma duka su zama Musulmi, ba wani abu ne na tada hankali ko fargaba ba. Abin yana bukatar dakewa ne kawai da kirmisisi na siyasa. Kuma idan muna bukatar abin koyi to abinda Ahmad Nasir El Rufai ya yi a jihar Kaduna ya ishe mu.
Wadan nan mutanen suna cin mu da buguzum ne kawai. Sun ci rabonsu kuma sun zo suna cin namu. Lokaci ya yi da za’a yi raba-dai-dai. Su rike tattalin arziki, mu rike siyasa. Wannan kuma zai taimaka mana fito da mutanen mu daga kangin fatara da jahilci.
Muna maraba da Tambuwalci a siyasar Nijeriya.