Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar fim
Gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.
A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta. Legit ta ruwaito.
Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda mace ta ke nema a wurin mijin aure.
Ta ce tana son namiji kyakkyawa mai tsoron Ubangiji
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ta furta cewa:
“Don Allah, ina son yin amfani da wannan damar in sanar da duniya cewa ina son in yi aure cikin gaggawa. Don haka kasaitaccen namiji ya bayyana kansa kuma ya sanya min zobe a hannuna. Abin da nake so tattare da shi shi ne ya kasance mai tsoron Ubangiji kuma kyakkyawa.
“Wajibi ne ya cancanta, ya kuma mallaki duk wani abu da ake so a wurin namiji. Kada ya kasance mai wata nakasa, shikenan abin da zan ce.”
Haifaffiyar Jihar Imo ce.
An zargi jarumar wacce ta koma fasto da soyayya da abokin sana’arta, Lucky Oparah, wanda ta musanta.
Asalinta haifaffiyar Owerri ce, Jihar Imo kuma bayan ta kammala karatunta na sakandare ta zarce Cibiyar Gudanarwa ta Fasaha (IMT), Enugu, inda ta yi karatun diploma a fannin jaridanci.
Ta fara sana’ar fim a shekarar 1994 inda ta fara da fim din ta na ‘Glamour Girls’.