Wasu ɓata gari sun cinnawa wani matashi wuta saboda canjin N100
Ana zargin wasu ‘yan acaɓa da cinnawa wani matashi wuta a jihar Legas. Shafin LIB ya rahoto
Matashin mutumin mai suna David, an yi masa dukan tsiya sannan aka cinna masa wuta wacce tayi sanadiyyar ajalin sa.
Ana zargin matashin sun samu saɓani da wani ɗan acaɓa
Ana zargin cewa David ya samu saɓani ne da wani ɗan acaɓa kan canjin naira 100. Hakan ya sanya faɗa barkewa tsakanin David da ɗan acaɓan.
Sauran abokan aikin ɗan acaɓan sun shiga cikin rigimar inda su ka yiwa David dukan tsiya har sai da ya sume.
David, yana kan hanyar sa ta komawa gida daga wajen shaƙatawa lokacin da lamarin ya auku a yankin Lekki Phase 1, jihar Lagos.
An saka bidiyon lamarin a shafin Twitter
Bidiyon lamarin da aka saka a shafin Twitter ya nuna David a kwance a ƙasa da tayar mota na ci a jikin sa. Sannan mutanen da su ka farmake sa su ka sanya wa wutar man fetur, wanda hakan ya sanya wutar ta ƙaru.
David dai ya sha kashi ne tare da wasu abokan sa a hannun mutanen da har yanzu baa san ko su waye ba.
Abokan David, ma su suna Frank da Philip ana duba lafiyar su a wani asibiti da baa bayyana sunan sa ba. Labarunhausa na wallafa