google-site-verification=WmtThtgKMuimwQoXo8Cd4z9ZhII1jY-1XVfjGSvL5r8
Labarai

Tiktoker: Muhimman Abubuwan da ya kamata ku sani game da Rahama Sa’idu da aka kora daga makaranta

Wannan yarinyar da hotunanta ke kasa mai suna Rahama Sa’idu da labarin ta ya yadu a shafukan Sada Zumunta, bayan da ta fito a shafin ta na Instagram ta wallafa cewa wai an kore ta daga Makarantar Kimiyyar Koyon Aikin Jinya ta Jihar Kebbi, saboda kawai ta na amfani da shafukan Sada Zumunta na Yanar Gizo, wadda kuma labarin ya fantsama duniya a haka, karya ta ke game da abun da ta shaidawa duniya kan dalilin korar ta daga Makarantar nan.fitaccen marubucin nan kuma dan jarida Ahmad Nagudu ne ya rubuta ko ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Asalin sunan ta shine Ramatu, ba kamar yadda ta canja ta mayar da shi Rahama ba. Iyayen ta Yarbawa ne da su ka fito daga Ibadan ta Jihar Oyo, amma a kauyen Ribah aka haife ta da ke Karamar Hukumar Zuru ta Jihar Kebbi. A nan ta tashi ta girma, kowa na ta a can ya ke. Mahaifin ta sana’ar tukin mota ya ke yi, duk da ya taba wasu ayyukan kamin wannan.Tiktoker: Muhimman Abubuwan da ya kamata ku sani game da Rahama Sa'idu da naka kora daga makaranta

Duk da ina ganin sunan yarinyar nan Rahama kuma Sa’idu, wallahi ban taɓa zato ko daukar ta a musulma ba a iya sanin da na yi mata.

Domin kwata-kwata tsarin rayuwar ta bai yi kama da na ‘ya ‘yan Musulmai masu mutunci ba. Kamar yadda na ke gani da ji, wallahi ko ni ne ta ke makarantar da na ke Shugabanci, sai na sallame ta. Domin barin ta a dai kan irin turbar da ta ke kai din nan, a hankali zai kwadaitawa wasu masu raunin zuciyar irin kazamar rayuwar da ta ke dabbakawa wadda babu Allah da Annabi da tunanin makoma a cikin sa.

Duk da ni a waje na, daga irin tambelen da na ga ta ta ke yi a shafukan Sada Zumunta; Instagram da Tiktok, ban ma yadda ta na makaranta ba, domin karatun kirki da ake neman makoma a cikin sa, ba zai hadu waje daya da irin wannan rayuwar shashancin na ta ba. Kuma ko da ta na makarantar ma, ni ban yadda ta na zama a cikin ta kamar sauran daliban kirki ba.

Domin wannan yarinyar da ku ke gani, kullum ita ce Abuja, Kaduna, Kano, wani lokaci har Lagos, me ta ke zuwa yi can? Ko za ta ce ta na da ƴan uwa ko dangi a can duka ne? Idan ma ta na da su, da yawan Bidiyoyin da ta ke yi ta na wallafawa a Tiktok, a dakunan Hotels ta ke yin su a garuruwa daban-daban da ta ke zuwa.

Ta na mace, yarinya karama haka, kuma musulma, wannan halin kirki ko tarbiyya ne? Babu wani mai hankali da za ta yaudara da wannan kukan munafurci da rainin wayon na ta! She’s doing all these just to call people attentions on her. While, ba ta fito ta gayawa duniya ita na ta laifin ba. Ta na Musulma, yar Musulmai, amma kullum kai babu dankwali, ta na ta gantali da jiki a bude, sannan ta na zaton za a zuba ido a bar ta, ta ci gaba da yi ko? To, idan iyayen ta sun kasa kula da ita da tarbiyyar ta, da sa ido akan abubuwan da ta ke yi, ita Hukumar makaranta, ba za ta saka ido ba haka nan ba. Duk da ma su ba a kan wannan su ka dauki mataki a kan ta ba.Tiktoker: Muhimman Abubuwan da ya kamata ku sani game da Rahama Sa'idu da naka kora daga makaranta

Domin ba iya karatu kadai ake koya a makaranta ba, har da tarbiyya. Wannan kuma shine hukuncin da ya dace da ita da duk wata ire-iren ta kawai.

Yarinya ce karama wadda sakacin iyayen da su ka haife ta da su ke rayuwa akan doron wayewar Boko da rashin tasirantar ta da Addini akan zamani ya jawo sauyawa da gurbacewar ta cikin kankanin lokaci ta zama haka. Kuma Social Media; musamman Tiktok da Instagram ya taka rawa da taimakawa wajen kara fandarar da ita da bude mata ido ta hanyar haduwa da gogaggun kadangarun bariki da su ka kwashe kayan su daga gaban Annabi da dokokin Allah wadda ta kara lalacewa ta dalilin wannan ma.

A gefe guda kuma, tun da ta ce ta na business, wanne business ne yarinya karama kamar wannan za ta ke yi alhalin ɗalibar makaranta ta ke? Wa ya saka ta a makaranta ya ke biya mata kudin karatun tun da farko? Wai wane business ne ma wannan ne? Bayan mun san irin lokaci da ba da himma da fannin karatun koyan aikin jinya ya ke da bukata fiye ya ke da saura fannonin karatun!

To, idan ma har hakan ne, ta je ta ci-gaba da business din ta mana kawai, tun da shine abun da ta ke rufawa kan ta asiri da iyaye da kannen nan ta kamar yadda ta ke ikirarin. Kamar shine da abun da ya fi dacewa da ke ba karatu ba, karatun ma na Nursing.Tiktoker: Muhimman Abubuwan da ya kamata ku sani game da Rahama Sa'idu da naka kora daga makaranta

Domin dama ai da irin wannan raye-rayen ta ke samun kwastoma a business din na ta da ba mu sani ba ai ko? Mtsssw! Shi kuma karatun tun da dama ba kudi ta ke samu da shi ba ba, to meye na damuwa don an kore ta daga shi? Ƴar rainin hankali kawai.

To, daga ƙarshe ma dai, ga nan Hukumar Makarantar ta fito ta bayyana gaskiyar lamarin abun da ke faruwa. Wadda dama sai da na yi wannnan tunanin a cikin rubutun nan a sama.

Babu ta yadda za ka bibiyi shafukan ta, ka ga irin rayuwar da ta daukarwa kan ta, ta ke yi, sannan a ce za ta mayar da hankali a kan karatu ko neman ilmi. Zai yi matuƙar wahala wannan kam wallahi. Don layin ba ma ɗaya ba ne. Tiktoker: Muhimman Abubuwan da ya kamata ku sani game da Rahama Sa'idu da naka kora daga makaranta

Bayyanar da tsiraici, bibiyar waƙoƙin mawaƙa marasa tarbiyya, yan Kudu a mabambantan wurare cikin shigar banza da sauran su. Kuma duka bidiyoyin da ta ke yi, babu wadda za ka gan ta da shigar mutunci ko a makaranta da ke nuna alamar ko karatu ko ta ke yi. Wadda wannan ke nuna karatun ba shi da wani muhimmanci a gare ta.

Daga karshe, Jama’a, an kori wannan yarinyar Rahama Sa’idu daga makarantar Kimiyyar Koyon Aikin Jinya na Jihar Kebbi ne sakamakon faduwa jarrabawa da ta yi, kuma ba ta zo ta gyara ba. Daga nan sai da ta shafe kusan wata 5 ba ta shiga Aji da sunan karatu ba, alhalin ta na matsayin ɗalibar makarantar, wannan ya sa Hukumar Makarantar su ka rubuta takardar kora su ka aika mata. Wadda dama kuma haka dokar irin wadannan makarantun koyan aikin lafiyar su ke. A kan abun da bai kai wannan ba ma, su kan yi kora balle na wannan.

Amma da ya ke gogaggiya ce a bariki, shine ta ke neman wawantar da tunanin mutane ta hanyar murde ainahin yadda gaskiyar lamarin ya ke, ta fitar da wani labarin ƙarya don ta jawo hankalin mutane da duniya zuwa kan ta. Wadda kuma har an samu wadanda su ka rufta cikin wannan tarkon yaudarar ta ta, har sun fito su na ta babatun yada da’awar wai a yi wa Rahama Adalci.

Adalcin me za a yi mata bayan ita ta kasa yi wa kan ta?

Makaryaciyar banza.

Ku yi hakuri da tsawon wannan rubutun nawa, tsohon tsimin Sayyadancin Islamiyya ne ya motsawa Malam Ahmad Alhaji Umar wadda ku ka fi sani da Ahmad Nagudu.

Kuma kun san dai yadda marubuci ya ke idan ya samu abun rubutu a kai ko? Musamman wadda ya ke a zahiri da ba sabon kirkira zai yi ba.

Na gode da lokacin ku na karantawa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button