Labarai

Na Dai Na Karuwanci Tun Bayan Da Wani Aljani Ya Daukeni Kwanan Gida-Inji Wata Karuwa Mai Murabus

Tace, “Ban taba tunanin zan daina karuwanci ba, domin harka ce mai kawo kudi da riba sosai tun ma ba ace mace tana da kyau da yarinta ba. Musamman ace ta iya kwalliya da rangwada.

” A dare daya nakan hada dubu 50 zuwa 100 na naira a mari ka tashi kawai (short time) banda kwana gida. Don haka ne sai abunda nake so nake ci, nake sakawa a jikini. Zancen saurayi ko soyayya bansanshi ba saboda ban taba yi ba”. Injita.
Ta ci gaba da cewa,” sai dai kwasam babu shiri na rantsai bani ba harkar karuwanci. Mata masu yi ma fatan su dai nake musu a kullum.

“Wata ranar asabar na fito kamar yadda na saba ina Kai goro ina kai mari a inda muke tsayawa maza suke zuwa su dauke mu,domin yin farautar kwastoma. Nayi shiga kusan akasarin jikina a waje yake. Sai ga wata gingimemiyar mota ta tsaya a gabana. Bayan na leko ne ya nuna na masa yana son na bishi gidansa mu kwana. A tsarina bana bin mutumin da bansanshi ba gidansa, amma saboda kyau mutumin nan ko musu haka ban masa ba. Cikin girmamawa ya fadamini ga abunda zai bani kudi ne masu tsoka da ya kamata idan na samesu ace na daina zina. Amma ni a wannan lokacin ba kudin bane a gabana kawai na kamu da sonshi ne nan take.

“Ya kaini shagon sayayya na sayi abunda nake so naci, muka kama hanyar zuwa gidansa. Wani katafaren gidane mai matukar kyau da kyalekyeli. Muna dosan gidan na tsorata har sai daya gane. Nan yace mini kada na damu bazai cutar dani ba.
A takaice, muka kwanta bacci bayan mun gama yin zina. Wajen 5 na asuba sai nace bari na tashi domin na koma gida kamin gari ya gama wayewa saboda irin wannan shigar danayi. Ai kuwa ina bude idanuwa na sai na ganni a tsakiyar makabarta ina kwance ni kadai. Ga kudi an ajiye mini kusa da jakata. Ga kuma duk kayayyakin dana sayo naci a inda na zauna na ci. A lokacin tsoro ya kamani, na dauki kudin da jakar da kyar na samu hanyar fita. Na kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu kamin nan na samu kaina da kyar. Wannan yasa nayi alkawarin na daina karuwanci har a bada.” Ta kammala.

Wannan dai wani darasi ne na musamman daya kamata mata masu wannan harkar su dauka daga wannan labarin da uwar bari ya sata rabuwa da aikin ta zubar.daga tonga abdul tonga.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button