Labarai

Shugaba Muhammadu Ya Yabawa Irin Hakuri Da Juriya Da Bukola Saraki Yayi A Shari’arsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da wanke shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da kotun koli ta yi.
Shugaban ya ce duk da kalubalen da bangaren shari’ar kasar ke fuskanta amma hakan ya nuna bangaren na aiki sosai, kuma babu wanda za a bari ya karya tsarin.
Shugaban ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu.

“Na ga shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya bi tafarki mafi wahala na bin matakan shari’a, ya jure, kuma daga karshe kotun koli ta ce ba ya da laifi” in ji shugaban.
Ya kara da cewa: “Akwai wasu lokutta da dama da wasu mutane cikin rashin tunani suke neman kawo lalaci ga bangaren shari’a duk don su kare kansu, maimakon mayar da hankali ga bin matakan da za su wanke kansu.”

A ranar Juma’a ne kotun kolin Najeriya ta wanke Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa, karar da gwamnatin Buhari ta shigar a gaban kotu.
Tun a watan Satumban 2015 ne gwamnati ta shigar da karar Saraki kan tuhume-tuhume 18 na yin karya wajen bayyana abin da ya mallaka.
Tun lokacin Saraki ke safa da marwa zuwa kotu tare da kuma gudanar da aikin jagorantar majalisa.

Amma a martaninsa, shugaba Buhari ya kwatanta shari’ar Saraki da shari’arsa da ya dauki lokaci yana zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zabukan da yake shan kaye.
“Abin na yi ke nan a zabuka uku da aka zalunce ni, kafin Allah ya ba ni damar tsayawa takara a karo na hudu.” Buhari ya ce yadda Saraki ya dinga yawo tun daga karamar kotu zuwa kotu mafi girma a Najeriya ya zama babban misali da ya kamata dukkanin ‘yan Najeriya su yi koyi da shi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button