An kashe wani dalibi a Jami’ar FUDMA akan rikicin soyayya
![An kashe wani dalibi a Jami'ar FUDMA akan rikicin soyayya](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/09/IMG_20230930_090138.jpg?fit=1080%2C810&ssl=1)
![An kashe wani dalibi a Jami'ar FUDMA akan rikicin soyayya](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/09/IMG_20230930_090138.jpg?fit=1080%2C810&ssl=1)
Wannan matashin da kuke gani sunan shi Abubakar Nasir Barda, yana aji 2 a jami’ar gwamnatin tarayya ta FUDMA da ke garin Dutsinma a jihar Katsina, matashin dan gwagwarmaya Comr Nura siniya ya wallafa labarin a shafinsa na sada zumunta facebook.
Wanda ake zargin wasu ɗalibai Inyàmúrái àbokan karatunsa sun kàshé shi ta hanyar yi màshi bugun tàron dangi sakamakon takun saƙar da ya shiga tsakaninsu akan rikicin soyayyar wata ɗaliba mai suna Joy wacce ya samu gurbi a zuciyarta, inda suka yi ta búgunsà da katakai da itatuwa sai da ya mutu har lahira.
![An kashe wani dalibi a Jami'ar FUDMA akan rikicin soyayya An kashe wani dalibi a Jami'ar FUDMA akan rikicin soyayya](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/09/IMG_20230930_090138.jpg?resize=300%2C225&ssl=1)

A bayanan da muka samu ɗaliban da ake zargi da kisan Abubakar, sun fasa masa kai saboda tsananin duka inda jini ya riƙa fita ta hanci ta baki har sai da ya faɗi ƙasa wanda daga bi sani aka kai shi asibitin makarantar, amma daga ƙarshe Allah ya karɓi ran shi.
Abubakar ya gamu da àjalinsa ne, a daidai lokacin da ya ke zana jarabawar ƙarshe ta aji biyu a jami’ar.
Wannan babban abin takaici ne da Allah wadai ga ɗaliban da suka yi wannan aika aikar ga Abubakar, wanda ya kamata ayi gaggawar bi mashi haƙƙinsa.
Da wannan muke kira ga mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakin hukunci ga waɗannan azzaluman ɗaliban mara sa imani da tausayi da suka yi mashi wannan aika aikar tare da biyan iyalansa diyya.
Muna Addu’ar Allah ya jiƙanshi da rahama ya gafarta masa yasa Aljannan ce makomarsa.