Uncategorized

Idan Kana Auren Mace Mai Karancin Shekaru Zaka Fiskanci Wadannan Abubuwan

Duk da yadda maza suke sha’awa da son auren mace mai karancin shekaru. Ba duka mazan bane kuma suke da illimin fahimtar yadda zasu zauna da irinsu ba.

Mace koda mai yawan shekaru ce zama da ita yana bukatar, hakuri, kawaici da kuma lanlami. Bare kuma mai karancin shekaru.
Yana da kyau duk wani namijin da yake da niyar auren mace mai karancin shekaru, ko yake auren irinta daya kwana da sanin zai iya fuskantar wadannan abubuwan kamar haka:

1: Kewar Gida: Ita amarya mai karancin shekaru a farkon watan data zo ta gidan mijin babu abunda zata matsa masa dashi Irin tana kewar gidansu. Wannan gidan nasu koda daga gidan kasa aka kaida gidan da aka shafe da kayan kawa sai ta nuna maka cewa ita fa tana kewar gida.
Zaku ma ta nuna maka tana son ganin iyayenta ko wasu kannenta ko yayyunta mafi kusanta da ita.

A duk lokacin da ka fiskanci irin wannan idan gari guda kake da iyayenta yi kokarin gayyato wata nata mai wayo da hankali ba irinta ba tazo su yini da ita. Idan kuma ba gari guda kuke ba bata wani lokacin da zakace mata zakuje. Yi kokarin hadata ta waya da mutanen data fi damuwa dasu.
Kada ka sake ka biye mata na amsa bukatarta na kaita gidansu. Da zaran ka biye mata hakan zata maida hakan ya zamemata dabi’a.

2: Bata Damu Da Ku Zauna Kuyi Hira Ba- Ita mace mai karancin shekaru ba damuwanta bane sai miji ya kasance kusa da ita irin kuna zaman hira din nan. Bama ta son a ganta kusa da miji bare aganta a jikin mijinta tana hira dashi.
Kallon talabijin ko wasa da yaran gida ko hira da wasu matan gida idan akwai su ya fiye mata zama tayi hira da mijinta.
Idan har wacce ka aura haka take. Kada ka bata rai da ita. Da duk randa kake son da zauna zaman hira da kai shigo mata da abunda take son ci. Idan mai son kallo ce ko abunda yayi kama da hakan samar mata tashar da take so kuma shirin data son gani. Sannu a hankali zata rika sabawa amma bada fushi na ko tilasta mata da gadaran kaine mijinta ba.

3: Marabtar Baki- Ana samun mata amare masu karancin shekaru da zasu iya baiwa baki wajen zama da abinci. Amma bazasu iya zama cikinsu suyi hira ba musamman idan bakin ba nata bane ba.
Wasu kuwa zasu fito su marabci bakin amma ko ruwa sai an tuna musu zasu kawo. Wasu kuwa shiga daki zasuyi su kunshe kodai saboda kunya ko saboda basu son ganin baki ko basu saba da ganin baki a gidajensu ba.

Idan wacce ka auro tana cikin wadannan da muka lissafa. Sai ka kiyaye irin bakin da zaka rika gayyatowa gidanka. Ma’ana ba bakin kunya bane bakine na kusa da kai. Dasu ne zaka koya mata yadda kake so ta rika karban baki. Amma kada ka saba da mata hayaniya a gaban baki saboda tayi wani abun ba daidai ba.
4:Kalamai Na Rashin Girmamawa-Duk da tana sonka. Dole ne sai kayi hakuri da wasu kalamai da zata rika furta makasu.

Ita babban mace takan tauna magana kamin ta furta shi wasu matan. Amma mata masu karancin shekaru suna iya furta duk wani abunda ya fito daga bakinta.
Kada kalamanta su bata maka rai. Duk wani kalmar data furta shi ba daidai ba ko ba akan ka’ida ba fahimtar da ita inda, yadda da lokacin da zata yi amfani dasu. Ka kuma nuna mata hakan cikin soyayya, kauna da lanlami zata dauka.

5: Jima’i- Babban matsalar da maza masu auren mata masu karancin shekaru suke fuskanta dasu shine Jima’i. Wasu matan basa yarda da mazansu har sai an kai wani matsayi ko lokaci kamin suke samun shigarsu.
Yanada da kyau ka sani duk wata mace koda ma babbace da bata taba Jima’i ba ana tsoratata da suna abun akwai zafi. Baya ga hakan kashi kadan ne cikin mata da suke jin dadin Jima’i a ranar farko. Koda kuwa ba zafi ko ciwo suka ji ba. Sannan sukansu mazan basa bin amaren nasu sannu a hankali a daren farko. Don haka idan ka wahalar da ita a farko tunda daman ba dadinsa ta sani ba gudunka kawai zata yi tayi.

Kada ka nunawa amaryarka mai karancin shekaru zalamarka na sai ka sadu da ita. Kada ta fahimci wannan shine hadafinka a duk dare. Idan har ka tashi yi kada ka mata abunda zai sata jin ciwo ko zafi koda kuwa ba dadi zata ji ba.
Wajen kokarin shawo kanta nuna mata alfanun yin Jima’i a tsakanin ma’aurata. Saurareta kaji hujjarta na gudun abun, domin bata amsar da zai gamsar da ita. Kada ka mata da karfi da takamar ai matarka ce.

Wadannan wasu abubuwa ne da duk namijin daya auri mace mai karancin shekaru zai iya fuskantar su. Da fatan za a yi amfani da shawaran da muka bayar.

Daga : Tonga Abdul Tonga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA