Hotuna: Malami ya raba kyautar motoci ƙirar Mercedes Benz GLK 14, Prado 8 da kuma Lexus SUVs 4 ga ƴan social media da yan siyasar kebbi
Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami SAN, ya raba kyautar motocin zamani na-gani-na-faɗa ga masu yaɗa manufarsa a kafafen sadarwa, ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen sa da kuma abokan siyasar sa a Jihar Kebbi.
Ɗaya da ga cikin waɗanda su ka amfana da motocin ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Malami ya taba motocin ne a wani ɓangare na shirye-shiryen baiyana takararsa ta gwamna a zaɓen 2023 a jihar.



DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa Ministan ya raba motocin ƙirar Marcedes-Benz GLK guda 14 ga ƴan barandan sa da ke yaɗa manufofinsa a kafafen sadarwa su 14.
Hakazalika abokansa ma su 4 sun samu kyautar motoci ƙirar Lexus LX 570.
Sai kuma Shugabannin gidauniyoyi da kungiyoyin goyon bayan Malami da a ka raba wa Prado SUV da kuma Toyota Hilux, inda kowannen su ya samu guda ɗaya.



![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






