Labarai

Yanzu – Yanzu : Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Ranar Sake Bude Portal Din N- Power

Advertisment

Ma’aikatar kula da ayyukan jin kai, da ibtila’i da kuma ci gaban Jama’a ta ce za ta fara rajistar kashi na uku na shirin N-Power a mako mai zuwa.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an yanke shawarar yin rajista a karo na uku na shirin ne biyo bayan shawarwari da kuma sake duba abubuwan da aka gabatar game da sake fasalin shirin don ingantaccen aiki.

Ta kuma yi bayanin cewa yin rijistar zai samar da dama ga dimbin matasan Najeriya don samun damar yin amfani da shirin, don inganta hangen nesan shugaban kasar na fitar da yan Najeriya miliyan 100 daga talauci.

Ma’aikatar ta ce wadanda ke sahun gaba a shirin (Batch A) za su fice daga 30 ga watan Yuni 2020, yayin da (Batch B) za su fice daga shirin a ranar 31 ga Yuli, 2020.

Advertisment

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa a Abuja ranar Juma’a ta hannun mataimakiyar daraktan yada labarai na ma’aikatar, Rhoda Iliya.

A cewar Ministan, Sadiya Farouq, “Mun fara sauye sauye masu amfani cikin tsare-tsaren A da B don saka su cikin tsarin koyarda sana’oin hannu na gwamnati da kuma hada hannu da bangarorin kamfanoni don jawo hankulan wasu daga cikin wanda sukayi nasara bayan kammala tantance su da sanya su cikin wasu damammaki.

Za’a bude shafin rigista a ranar 26 ga watan yuli, 2020, don baiwa kowa damar yin rigista.

“A matsayin wani bangare na sake fasalin Ma’aikatar don sa shirin ya fi dacewa, duk masu neman aikin dole ne su bayar da lambar tabbatar Bankin su (BVN) a lokacin yin rigistar su don tabbatar da tsarin zabe na gaskiya da nuna gaskiya.”

Daga karshe ta ce wanda suka ci gajiyar shirin ada, ba za su cancanci shiga cikin wannan tsarin  ba.

Shirin ya yi rijista ga mutane 500,000 zuwa yanzu tare da 200,000 daga tsarin A wanda ya fara a watan Satumbar 2016 da 300,000 daga tsarin B wanda ya fara a watan Agusta 2018.

Masu cin gajiyar shirin ba zasu wuce watanni 24 ba a cikin shirin kuma an baza su cikin manyan masana’antu wadanda suka hada da; noma, kiwon lafiya, ilimi, da haraji.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button