Labarai

Shahararren mawakin kasar Koriya ta Kudu ya yi aikin Ummara bayan ya Musulunta a 2020

Advertisment

Shauƙi ya tashi sosai lokacin da fitaccen mawaƙin nan na ƙasar Koriya ta Kudu, Daud Kim ya isa Makka domin gudanar da aikin Ummara.daily Nigerian hausa na ruwaito.

A shekarar 2020, Daud, wanda aka fi sani da Jay Kim, ya bayar da sanarwar ba zata a dandalinshi na sada zumunta cewa ya yanke shawarar shiga addinin Musulunci.

Da ga baya ya canza sunansa daga Jay zuwa Daud.

Bayan annobar korona, sai ya yanke shawarar shiga aikin Ummara, inda ya shiga shafinsa na Instagram ya riƙa saka hotuna da kuma wallafa saƙuna daban-daban.

Advertisment

Daga nan ne Dauda ya saka jerin hotunansa a Masallacin Harami a dakin Ka’aba da faifan bidiyo na kewayen masallacin.

“A karshe na zo Makka. Nine nafi kowa sa’a domin Allah SWT ya zabe ni ya kawo ni. Masha Allah,” ya wallafa a shafinsa.

Yace ya yi addu’a ga daukacin al’ummar musulmi na duniya.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button