Labarai
A’AJABI: Bakanon Da Jirgi Ya Tashi Ya Bari Ya Fara ‘Aikin Hajjinsa A Kano
Advertisment
Wani maniyyacin Jihar Kano da bai samu tashi a jirgin karshe ba zuwa kasar Saudiyya b ranar Alhamis ya ce zai yi Aikin Hajjinsa na bana a sansanin horar da alhazai da ke Jihar.
Idan za a iya tunawa, Aminiya ta rawaito muku yadda jirgin karshe ya bar shugaban Hukumar Jin-dadin Alhazai na Jihar Kano, Abba Danbatta, wasu Daraktocin hukumar da wasu maniyyata 745 a kasa, inda ba za su sami damar sauke farali ba a bana.
Jirgin na kamfanin Azman, wanda ya tashi wajen misalin karfe 3:40 na yammacin Alhamis, ya bar maniyyatan ne duk da karin wa’adin da kasar Saudiyya ta yi wa Najeriya.
Zaku iya shiga wannan link domin kallon hirar da ankayi da shi kai tsaye