Labarai

Wani Sojan Najeriya ya kashe kansa bayan an gano Yana aiki da Boko Haram/ISWAP

Wani sojan Najeriya da ke aiki da Bataliya ta Sojoji da ke Gaidam Lence Kofur Jibril ya harbe kansa bayan an gano shi tare da kama shi da laifin hada baki da Boko Haram/ISWAP a ci gaba da fafatawa tsakanin sojoji da mayakan.

Wata majiya ta bayyana cewa al’amura sun fara nuna shakku game da sojan a lokacin da ya bace daga wurin aikin sa na tsawon kwana biyu.

Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 21 ga watan Afrilu, an ga Sojan a cikin ‘yan ta’addan da suka kai hari a wata mashaya a garin Gaidam tare da kashe mutane kusan 9.

Ya ce, “A bisa haka ne, kwamandan sa, Laftanar Kanal Mikah, ya binciki wayarsa, aka gano shi a wani wuri a Gashua, cikin karamar hukumar Bade, mai tazarar daruruwan kilomita daga inda aka ajiye shi dan gudanar da aiki.

“an sake kai hari wata mashayar a Gashua, inda mutum daya ya mutu, wasu bakwai kuma suka jikkata, ana kyautata zaton Jubril na daya daga cikin wadanda suka kai harin,” in ji majiyar.

Ya bayyana cewa, nan take aka aika da sako zuwa sansanin Sojoji da ke Gashuwa tare da fadada bincike. Da safiyar Talata ne Jibrin ya canza kama, ya shiga motar safe zuwa jihar Gombe, wanda akan hanya ne sojoji suka kama shi a shingen bincike da ke Gashua.

An tattaro cewa bayan an kama Jubril tare da daure shi da mari a hanyarsa ta zuwa Geidam, ya yi aiki da kwarewarsa a matsayin mai koyar da sarrafa makami, ya kwace bindiga daga daya daga cikin masu rakiyarsa, ya ci karfin daya kuma ya tarwatsa kansa.

Abubuwan da suka bayyana lokacin da aka kama shi da tambayoyin da aka yi masa, sun kai ga kama wasu ‘yan’uwansa masu ta’addanci a a boye cikin sojojin.

Jibrin, dan ƙabilar Babur wanda yake dan karamar hukumar Biu, yana cikin Hukumar Leken Asiri kafin ya zama malamin koyar da sarrafa makamai a rundunar ta soji.

Daga:Aliyu Samba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button