Addini

[Bidiyo] Musulmin Kwarai zai Iya Auren Mace ‘Yar Soshiyal Midiya Wadda Take Saka Hotunanta Masu Nuna Tsiraicinta? – Dr Jabir Sani Maihula

Dr jabir sani Maihula yace abinda yakamata idan mutum yana abu ba dai dai ka kirashi kayi masa wa’azi kayi masa nasiha.

Idan kaga wata tana sanya hotunan a soshiyal midiya tana nuna tsirancinta kayi mata nasiha wannan abu da kike bai kamata kiji tsoron Allah ki daina yada hotunanki ko jikinki a soshiyal midiya.

Malam ya kara da cewa abu na farko kayi masa nasiha karka wani yazo neman aurenta kace a’a karka aureta wannan ba daidai bane ka gyara mata shine daidai.

Ko ba sanya hoto a soshiyal midiya ba duk wani abu da mutum yake ba daidai ba ka gyara masa kayi masa nasiha domin ka samu lada.

Amma baya hana a aure macen da ke sanya hotunanta a soshiyal midiya, Allah yasa mudace Amen.

Ga bidiyon nan kasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button