Addini

Sheikh Abduljabbar: Rundunar ‘yan sanda ta kama malamin na Jihar Kano Zuwa Gidan Yari

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa ta kama Malamin nan Sheik Abduljabbar Kabara.
Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya gaya mana cewa sun gurfanar da Sheik Abduljabbar a gaban kotun Kofar Kudu da ke kwaryar Birnin Kano a ranar Juma’a, bisa zargin ɓatamci ga addini da kuma tunzura jama’a.

Hoto : Facebook – A lokacin da aka tafi da shi

A cewarsa tuni alƙali ya aike da shi gidan yari.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar ta ce an gurfanar da Malamin ne, “wanda ya yi ƙaurin suna wajen ɓatanci ga manzon Allah da kuma Sahabbansa”, bayan da aka samu rahoton farko daga wurin ‘yan sanda da kuma ofishin kwamishinan shari’a wadanda suka shirya tuhume-tuhumen da ake yi wa Malamin.
Hoto : Facebook – A lokacin da aka tafi da shi

“An gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu da ke kofar kudu a ranar 16 ga watan Yuni, inda Alkali Ibrahim Sarki Yola, ya karanto masa laifukan da ake tuhumarsa da su wandanda suka haɗa da batanci ga addini da tunzura al’umma da kuma wasu sauran laifuka,” in ji sanarwar.
Kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 28 ga wannan watan na Yuli domin ci gaba da sauraron shari’ar.
malamin zai ci gaba da zama karkashin kulawar ‘yan sanda har zuwa ranar Litinin da za a kai shi gidan yari, kafin lokacin da za a ci gaba da sauraren shari’ar tasa.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Ina goyan bayan duk wani hukunci dakotu zata yankewa wannan malamin, domin kuwa ada ni magoyin bayansane amma yanzu nadawo daga rakiyarsa, donhaka ina mai rokon gwamnatin kano mai adalci da malamai masana addini dakuma alkalai masana shariar musulinci dasusa ido ayanke mishi hukunci dai dai da abin da ya aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button