Labarai

Ba wanda zai sake hawa jirgin ƙasa sai yana da lambar NIN – NRC

Fasinjojin da ke shirin hawa jirgin ƙasa su yi maza su tanadi lambar shaidar ɗan ƙasa, NIN da ga watan Mayu domin sai da shi za a shiga jirgin.

Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen kasa ta Ƙasa, NRC, Fidet Okhiria, ya bayyana haka ne a Abuja a yau Alhamis, inda ya baiyana cewa za a bukaci NIN ɗin ne domin inganta bayanan fasinjoji.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito a cewar sa, wannan matakin zai kuma inganta kariya da kuma tsaro na masu amfani da layin dogo.

“An fara ma aiwatar da tsarin haɗa fasinjoji da NIN ɗin su don inganta bayanan fasinjoji. Wannan matakin gwajin fasinjan zai fara a watan Mayu.

Hukumar NRC ta dakatar da jigilar jirgin na hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon harin da wasu mahara suka kai ranar 28 ga watan Maris, inda suka kashe da jikkata fasinjoji tare da yin garkuwa da wasu.

Okhiria ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tukuru domin ganin an ceto da kuma sako dukkan fasinjojin da aka sace.

Ya jaddada cewa fasinjoji 362 da ma’aikatan jirgin 20 ne ke cikin jirgin a lokacin da aka kai harin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button