Labarai

Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai na dala biliyan daya

Advertisment

Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan daya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.

A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.

Amurka ta ce daga yanzu Najeriya ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen sayen makamai daga wurin ta.

Daily Nigerian hausa ta ruwaito sai dai ana sa rai wannan batun zai dauki akalla shekaru biyar kafin a kammala shi – domin kuwa zai hada da horas da dakarun tsaron Najeriya kan yadda za su yi aiki da makaman da kuma kauce wa kai hari kan fararen-hula.

Advertisment

Wannan ne karo na biyu da Amurka ke sayar wa Najeriya makamai cikin shekaru biyar.

A baya gwamnatin Barack Obama ta ki sayar wa Najeriya makamai bisa zargin take hakkin dan adam.

Sai dai a shekarar 2017, gwamnatin Donald Trump ta amince ta sayar wa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12.

A shekarar da ta gabata ne aka kai jiragen Najeriya.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button