Labarai

Ta Kashe Kanta Saboda Mijinta Zai Kara Aure

Wata mata aure ta kashe kanta ta hanyar shan guba saboda mijinta zai yi mata kishiya.

Matar wadda suke da ’ya’ya biyu tare da mijin nata ta kwankwadi gubar ce bayan sun samu sabani da shi kan shirinsa na kara aure, saboda Musulunci bai hana ba.

Wani dan uwan mijin marigayiyar mai suna Alhaji Lagbe Araoje, ya ce, “Ranar Litinin da misalin karfe 10 na safe ta samu sabani da mijinta a waje, amma aka sasanta su. Daga baya mijin nata ya ba ta wata waya da take so. aminiya ta ruwaito.

“Bayan ’yan mintoci sai aka gan shi ya fito daga gidan yana kuka cewa matarsa tana amai.

“A hanyarmu ta kai ta asibiti ta rika rokon shi ya yafe mata, tana bayyana cewa wani garin hoda da ake kira DDT ko Sniper ta sha.

“Daga baya Allah Ya yi mata cikawa a asibiti da misalin karfe 12 na rana,” a Babban Asibitin Ilori da ke Jihar Kwara.

Wani mai kemis a yankin da abin ya faru ya tabbatar cewa marigayiyar ta sayi Sniper a kantinsa.

Amma wata wadda ta ce abokiyar karatun mamaciyar ce, ta yi zargin cewa surukar mai rasuwar ce ta sanya mata guba, saboda sun samu sabani kan addinin da marigayiyar wadda Kirista ce.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button