Labarai

Boka ya mallake ta : Taje wajen boka neman maganin mallakar Maza, ya gamsar da ita

Wata budurwa ne Musulma mai karancin shekaru kyakkyawan na gaban misali, iyayenta sun tura ta karatu a Kwaleji, anan ta hadu da Malaman Kwaleji guda hudu suka bata mata rayuwa, ma’ana suna fasikanci da ita

Daya daga cikin Malaman sai ya lura ta fara juya masa baya, sai yake tambayarta me yake faruwa?, sai bata boye masa ta fara bashi labari kamar haka, Datti Assalafiy ne ya ruwaito labarin

Na je wani kauye bikin ‘yan uwan mu, sai na je gurin wani mai magani wato boka matashi ne domin ya bani asirin da zan mallaki maza su dinga bani kudi isassu, to amma bokan sai yayi amfani da wannan damar ya kwanta dani

Tace tunda bokan ya kwanta da ita ta dena jin dadin wani namiji imba wannan bokan ba, ta kan bar gari ta tafi gurin bokan, wani lokaci ita take kiran bokan ya biyota gari don ya sadu da ita

To shine sai Malamin ya kawo karan bokan gurin wani babban jami’in ‘yan sanda saboda kishi (ku ji wani irin karfin hali fa), ya bukaci ayi masa binciken a boye kar iyayen yarinyar su sani, kuma shima fa Malamin fasikanci yake da yarinyar

An je an kama boka, kuma bai musa ba ya amince da laifinsa, yace kuma shi ba asiri ya mata don ya mallaketa ba, kun san ‘yan sanda da tambaya, an tambayi yarinyar cikin wadanda suke kwanciya da ita wa yafi gamsar da ita? sai tace tabbas boka ne tafi jin dadin saduwa da shi

Sai aka fara batun gwaji, ana zuwa Asibiti aka gwadata sai ga ciki ya bayyana na wata biyu, Malamin ya kaita wani guri aka zubar da cikin, kuma ‘yan sanda sun shiga tsakaninta da boka, Malamin shi ya dauki nauyin komai aka kashe case din gaban ‘yan sanda, anyi haka duk ba tare da sanin iyayen yarinyar ba

Idan kun ga yarinyar kyakkyawace kamar ita ta yi kanta saboda da kyau, amma ku duba yadda ta tarwatsa rayuwarta, kuma a haka wani zai zo ya aura yayi zaton budurwa ya aura, kuma mafi akasarin irin wannan yara da suka saba kwanciya da maza ko sunyi aure ba denawa suke ba

Iyaye musamman iyaye mata ku ji tsoron Allah, kina uwa ya za’ayi ‘yarki tayi ciki har ya kai wata biyu baki sani ba? menene amfaninki to?

Ya zama wajibi iyaye su zama masu saka ido da bincike akan ‘ya’yansu musamman mata da suka kai aure

A matsayinki na Uwa
(1) Idan kin ga ‘yarki ta canza waya dole ki tambaya???
(2) Idan kin ga ‘yarki ta canza suturu dole ki tambaya???
(3) Idan kin ga ‘yarki da kudi dole ki tambaya a ina ta samun kudin kuma kibi diddigi.
(4) Ki kasance mai karban wayanta kina bincike a lokacin da batayi tsammani ba.
(5) Ki kasance mai lura da lokacin da ‘yarki take jinin al’alada, ki mata binciken kwakwaf idan an samu karin kwana na al’ada
(6) Idan da hali har matucin ‘yarki ki kasance mai yawan bincikawa don tabbatar da yanayinsa
(7) Sannan a dage da yiwa yara ‘yan mata addu’ah, a rabasu da abokai ko kawayen banza
(8) Ki yiwa ‘yarki horo akan cire rai daga kwadayin abin duniya da son kudi da kyalkyali

Allah Ya karemu, Ya kare mana ‘ya’yanmu daga fitinar karshen zamani

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button