Labarai

Iyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

Advertisment

Jama’a sun tallafawa wata budurwa wacce iyayenta suka fatattaketa bayan ta haifa musu jaririn balarabe bayan ta dawo daga Saudiyya, Legit.ng ta ruwaito.

Kamar yadda wata Judy Oricho mai tallafawa masu kananun karfi ta bayyana a shafinta na Facebook, wanda Anna Awuor mai shekaru 29 ta fuskanci cin zarafi ne daga wanda take aiki karkashinsa, daga nan ta samu ciki.

Bayan fahimtar ta kusa haihuwa ne aka mayar da ita Kenya. Daga bisani ta haihu wanda hakan yayi sanadiyyar da aka fatattake ta da jaririn balaraben da ta haifia,” inji Oricho.

Ganin hakan ne yasa ta nufi Migori tana neman tallafin wata ‘yar uwarta, ashe itama ta tashi. Hakan yasa ta nufi sansanin Migori don neman taimako.Iyayen budurwa sun fatattake ta bayan ta haifa musu jaririn balarabe daga dawowa Saudiyya yin aikatau

Advertisment

“Tana neman ko wanne irin taimako, abinci, suttura da kuma wurin kwana tare da jaririnta,” a cewar Oricho.

Ta yi nasarar samun taimakon don mazauna Kenya da dama dun tausaya mata wanda hakan yasa wata kungiya ta tallafa mata.

“Nagode sosai, kuma ina farincikin sanar da ku cewa an kai kuka akan lamarin ga kungiyar Harvest Hope of Africa wadanda suka amshe ta da yaron nata,” inji Oricho.

 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button