Labarai

Yadda na hadu da dirarriyar mata ta daga yin tsokaci karkashin wata wallafar Facebook

  • Wani matashi, Olayede Godwin, ya labarta yadda kafar sada zumuntar zamani ta taimaka mishi wurin samun matar da ya aura
  • Hirar ma’auratan ta farko ta fara ne a bangaren tsokacin wallafar Legit.ng na Facebook, inda suka fara hirarraki
  • Basu kai shekara da sanin juna ba, masoyan suka karfafa soyayyar su, sannan sukayi aure a watan Maris din shekarar 2022

Wani dan Najeriya, a wani sako da ya tura wa Legit.ng ya bayyana yadda ya hadu da matarsa, Talatu Precious Mohammed Akoa.
Oloyede ya bayar da labarin yadda ya hadu da matarsa a sashin tsokaci na Facebook, karkashin wallafar da Legit.ng tayi.

Ya kara da bayar da labarin yadda a wurin tsokacin ne suka fara magana. Mata da mijin sun hadu karkashin wallafa a Facebook.

“Mun hadu, gami da yin aure bayan watanni uku,” kamar yadda ya shaida.

Kaddara ta hada su a wajen shagalin biki. Inda a nan ne suka yimusayar Lamba.
Haka zalika, matashin ya turo da tsala-tsalan hotunan da suka dauka kafin aure.
Wani bangare daga cikin sakon sa na nuna:

“A zahirin gaskiya, mun hadu a Facebook ne, kuma hirar mu ta farko akan wata wallafa da kuka yi ce.
“Bazan iya tunawa da wallafar ba. Bayan watanni uku muka hadu a wani biki, inda muka yi musayar lamba…”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button