Labarai

Batun dubu-dubu bayan yanzu an cika Shekara guda masoya buhari sunyi wa Rarara Allah ya Isa

A yau goma ga watan tara 9/10/2021 aka Cika Shekara ‘daya cif-cif da mawaki Dauda kahutu Rarara ya karbi naira dubu dubu daga hannun ‘yan Nageriya masoya Buhari
da nufin zaiyiwa Shugaba Muhammadu Buhari wata Mai taken BUHARI SUNANSA KAINUWA, Lamarin daya ja Hankalin ‘yan Nageriya masoya Buhari sukayi ta faman angiza dubu dubu a account lambar Kwamfanin mawakin Mai suna Rarara Multimedia LTD Rarara yayi alkawarin zaiyi wakar ne idan ‘yan Nageriya Suka biyashi kudin wakar.
Jaridar mikiya ga yadda ta kawo rahoton cikin jikin hoto inda wasu je masa tofin Allah tsine.

Batun dubu-dubu bayan yau an cika Shekara guda masoya buhari sunyi wa Rarara Allah ya Isa.

 
Rahotanni sun tabbatar da Cewa mawakin ya Samu tarin Ku’di masu yawa amma ya zuwa yanzu Shekara guda Sabuwar wakar Bata fito ba Lamarin dayasa wasu daga cikin masoya Buhari da Suka turawa mawakin kudinsu Suka Fara zagin mawakin tare da allah ya Isa tare da Cewa mawakin yaci amanarsu.
wasu kuma na Cewa a Kara hakuri haryanzu Rarara baice ba zaiyi wakar ba watakila Yana can Yana tsarata ne.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button