Labarai

Ina Mamakin Yadda Na Zama Dan Bindiga — cewar Bello Turji

Advertisment
Ina Mamakin Yadda Na Zama Dan Bindiga — cewar Bello Turji

Kasurgumin dan bindigar nan na Jihar Zamfara, Bello Turji, wanda ya shahara wajen garkuwa da mutane ya bayyana cewa shi kansa yana mamakin kasancewarsa dan bindiga.kamar yadda aminiya trust na ruwaito

Bello Turji, wanda ake zargi da yawancin ta’asar da ake aikatawa a yankin Arewa maso Yammacin kasar, ya  bayyana hakan ne a cikin hirarsa da shahararren ma’aikacin jaridar  Daily Trust, Abdulaziz Abdulaziz.

A cewarsa, da a shekarun baya idan aka ce zai zama shahararren dan bindiga ba zai taba yarda ba.

Ya ce a lokutan baya yana zuwa wurin sarkin Shinkafi kuma shima sarkin Shinkafi ya san shi, kuma yana zuwa har gurinsa.

A wancan lokacin inda za a ce zan zama rikakken dan bindiga, saboda kowa yasan mu Fulani ba barayin shanu ba ne, amma yadda ake mana ne ya sa muma dole mu ka sauya.

Ya kara da cewa, ayyukan ‘yan sa kai na daga cikin abubuwan da suka kara ta’azzara wannan rikici na ’yan bindiga tare da tursasa shi da sauran matasa zama ’yan ta’adda.

Ba na yi wa mata fyade

 

Don gane da zargin cewa kuma yana yi wa mata fyade, ya ce mutane ne kawai ke fadin son zuciyarsu.

Turji ya ce kowa na iya fadin abin da ya ga dama, amma abin da ya sani shi ne, shi ba ya fyade, yana mai cewa akwai mata a inda yake.

Ya ce da yana fyade, da ya fara da matan da ke inda yake a yanzu haka.

“Idan mata ne ai gasu nan ba sai na je na yi garkuwa da su ba tukunna zan yi amfani da su.

“Yanzu duk laifukan fyaden da ake samu misali a Kano nan ma Turji ne, to ka gani wannan ai ba sai an yi wa mutum wani karin bayani ba”

Sources :Aminiya trust

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button