Labarai

[Bidiyo] Yadda wani Matashi Yace baya Kaunar Mahaifiyarsa

Advertisment

Assalamu alaikum warahamatullah ina sallama irin ta addinin musulunci wannan wata kissa ce wanda wani matashi ake aibanta shi da ce masa kai can dan mai ido daya.

Yaron har yaji a zuciyarsa baison mahaifiyarsa wai missa mahaifiyarsa take da mai ido daya har takai yaga yakamata ya bar ganin yace yaje can inda ba’a san shi ba.

Kawai ya kama hanya ya tafi ana nan ana sai wata rana lokacin rasuwarta ta rubuta wasika ta sanya a ambulon tace dan Allah kada kowa ya bude wannan abari har sai ɗan ta yazo a bashi ya karanta.

Allah yayiwa wannan baiwa Allah rasuwa anka kirashi anka gayamasa cewa mahaifiyarsa ta rasu yaje kuje kuyi mata suruta da sallah Ni ba zanzo ba sai mutane sunka a’a akwai wasiyyar da ta barmasa.

Advertisment

Yaron ya dauka wata dunkiya ce ta bayar wasiyya sai yaron yazo a guje da yazo sai ya bude takarda bayan ya karanta sai ya fashe da kuka mi nene a cikin takarda abinda mahaifiyarsa ta rubuta a ciki shine.

Ɗana ka gujeni saboda mutane sun aibataka akan mahaifiyarka mai ido daya to ga yadda ankayi nake da ido daya.

Kana yaro dan shekara biyu kana wasa da kara yazo na karbe karan a hannunka sai ka tsokalin karen a idona idona ya tsiyaye kaji sanadiyyar rashin idona.

Wato a takaice kaine sanadiyyar mai ido daya”

 

Allahu Akbar yayi ta kuka yayi ta kuka yana tunanin ya zai nema afuwa ko gafara ina bata nan ta riga ta tafi sakamakon idon da yayi tafi shima idonsa ya tsiyaye shima ya zamo mai ido daya.

Bayan shekaru biyar ya nemi yan uwan wannan matar da ta rasu wasu makwabtanta ya basu hakuri kuma yazo musu da ‘ya’ya guda ukku wanda Allah ya azurta su da shi kuma dukkansu kuma masu ido daya Allahu Akbar.

Ina masu jin kunyar su nuna Mahaifiyarsu wannan ce mahaifiyata, wani yanajin kunya ya nunawa abokansa mahaifiyarsa, mahaifiya ta wuce wannan Allah yasa muna masu biyayya ga iyayenmu.

Wasallama warahamatullah wabarakihu.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button