LabaraiUncategorized

Allah yayiwa Bashir tofa rasuwa daya daga ciki dattawan arewa

Allah yayiwa Bashir tofa Rasuwa daya daga ciki dattawan arewa
Alhaji Bashar Tofa

Allah Ya yi wa Alhaji Bashir Othman Tofa, tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a tutar jam’iyyar NRC kuma ɗaya daga cikin fitattun dattawa a arewacin ƙasar, rasuwa.
Ya rasu ne a Asubahin ranar Litinin yana da shekara 74 a duniya bayan yayi fama da gajeruwar jinya.
Kamar yadda labarai24 na ruwaito za a sanar da lokaci da gurin da za a yi jana’izar sa nan gaba kaɗan.
Tarihin siyasar Najeriya ba zai taba cika ba tare da an ambato Alhaji Bashir Usman Tofa, musamman kan abin da ya faru a shekarar 1993 lokacin zaben shugaban kasa.
Alhaji Bashir Tofa dai shi ne dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar National Republican Convention wato NRC, a zaben da gwamnatin mulkin sojin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta shirya shi.
Wanene Alhaji Bashir Othman Tofa?
An haife shi a ranar 20 ga watan Yuli shekarar 1947, a garin Tofa na jihar Kano. Ya yi karatun firamare a makarantar Shahuci, daga nan ya ci gaba da karatu a City da ke jihar Kano.
Daga shekarar 1962-1966 ya yi karatu a kwalejin gundumar Kano. Bayan kammala karatun ya yi aiki da kamfanin Inshora na Royal Exchange daga 1967-1968.
A shekarar 1970-1973 ya yi karatu a kwalejin birnin London.
Alhaji Bashir Tofa ya tsunduma cikin siyasa ne a shekarar 1976 a lokacin da yake Kansilan karamar hukumarsa wato dawakin Tofa, shekara daya bayan nan aka zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar karamar hukumarsa.
A lokacin jamhuriya ta biyu, ya rike mukamin sakataren jam’iyyar NPN reshen jihar Kano, daga bisani ya zama sakataren kudin jam’iyyar.
A lokacin jamhuriya ta uku a shekarar 1990 Alhaji Bashir Tofa ya shiga jam’iyyar NRC.
Shekara uku bayan nan a lokacin da gwamnatin mulkin soja da Janar Badamasi Babangida ya jagoranta aka zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NRC da ya fito da jihar Kano.
A lokacin zaben fitar da gwani, ya kayar da Pere Ajunwa da Joe Nwodo da Dalhatu Tafida.
A lokacin babban aminin shugaban jami’an tsaron Najeriya wato Halilu Akilu.
A lokacin wanda suke takara tare da har da wani dan kabilar Igbo wato Sylvester Ugoh tsohon gwamnan bankin Biafra, dan jam’iyyar National Party of Nigeria NPN.
A lokacin zaben shugaban kasa ne Tofa ya sha kaye a hannun abokin karawarsa Moshood Kashimawo Olawale Abiola, dan kabilar Yoruba da ya fito daga kudancin Najeriya.
Sai dai kuma gabannin sanar da sakamakon zaben ne, gwamnatin Ibrahim Babangida ta sanar da soke shi.
A cewar gwamnati an tafka magudi a lokacin zaben.
A shekarar ne aka tilaswa Janar Babangida ya sauka daga mukami bayan zanga-zangar da aka yi na bukatar sanin sakamakon zaben.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA