Labarai

Kotu ta kori gwamnan Ebonyi sakamakon sauya sheƙa zuwa APC

Kotu ta kori gwamnan Ebonyi sakamakon sauya sheƙa zuwa APC
Babbar Kotun Taraiya a Abuja ta kori Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi da Mataimakin sa, Eric Kelechi Igwe sakamakon sauya sheƙa da ga Jami’yar PDP zuwa APC.
Da ya ke yanke hukunci a yau Talata, alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce ƙuri’u 393, 042 da Umahi ya samu a zaɓen gwamna na 2019 na PDP ne ba na APC ba.
Ya ƙara da cewa tunda Umahi da Mataimakin sa sun yi kaura zuwa APC, to ba zai yiwu su zauna a ka doron ƙuri’un da su ka samu a ƙarƙashin PDP ba.
Alƙalin ya ce, idan a ka yi la’akari da zaben 2019 ɗin, ofishin gwamnan da na maitaimakin sa ba na APC ba ne na PDP ne.
Sannan alƙalin ya ƙara da cewa dole jam’iyar PDP ce mamallakiyar ƙuri’un da masu zaɓe a Ebonyi su ka kaɗa mata a zaben 2019, inda ya ce babu yadda za a yi APC ta handime waɗannan ƙuri’un.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button