[Bidiyo] Mai unguwa ya daure ɗansa yaro mai shekaru 4 da sarka babu abinci har sai da ya kusan mutuwa a Katsina
Wasu ma’aurata a garin Faru na karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun hada baki sun yi ma wani yaro mai shekaru 5 a duniya daurin mutuwa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke gabatar da ma’auratan ga manema labarai.
Shi dai yaron, kamar yadda Katsina Post ta samu da ne ga tsohuwar matar mijin wadda suka rabu da ita shekarun da suka gabata.
Da yake karin haske kan lamarin, SP Gambo Isah ya ce jami’an yan sanda sun samu labarin halin da yaron yake ciki ne bayan da wata ‘yar uwar sa ta je gidan ta ga halin da yake ciki.
Ya kara cewa daga nan jami’an yan sandan suka kama ma’auratan tare da kai yaron asibiti.



Magidancin wanda shine mai unguwar kauyen na Faru tare da sabuwar matar sa dukkan su sun ansa laifin su.
SP Gambo Isah ya tabbatar da cewar za’a gurfanar da mahaifin yaron da matar ta shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A wani labarin mai kama da wannan, rundunar ‘yan sandan ta kama wani mutum daga gundumar Karaduwa ta karamar hukumar Matazu bisa laifin fatauci da siyar da ganyen wiwi fili kamar yana saida gyada.
Wanda ake zargin dai ya amsa laifin sa kuma Kakakin rundunar yan sandan, SP Gambo Isah ya ce za su gurfanar da shi gaban kotu da sun gama bincike.


