Labarai
Muna Rokon ‘Yan Nigeria Su Kara Hakuri ~ Buhari
Advertisment
Shugaba Muhammadiu Buhari na Najeriya ya roƙi ‘yan ƙasar da su ƙara haƙuri game da matsalolin tsaro da ake fuskanta, inda ya ce suna “bakin ƙoƙarinsu wurin sayo ƙarin makamai” don ƙarfafa ayyukan tsaro.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafukan zumunta, yana mai cewa tuni suka sayo wasu makaman, ana tantance wasu a gaɓar ruwa sannan kuma ana ƙera wasu.
“Muna matuƙar ƙoƙari wurin tabbatar da cewa mun bunƙasa harkokin tsaro a wasu sassa na Najeriya kuma daga cikin ƙoƙarin muna kashe kuɗi masu yawa wurin sayen makamai,” in ji Buhari.
“Ina roƙon a ƙara haƙuri kan maganar sayen makamai musamman saboda tasirin annobar korona kan ƙasashen da ke samar da su. Sannan idan kayan aikin sun iso, sai mun bai wa jami’an tsaro horo kafin fara amfani da su.”
A makon da ya gabata an kashe mutum aƙalla 30 a Kudancin Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar a rikicin ƙabilanci da ‘yan fashin daji da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Kazalika jihohin Katsina – mahaifar Buhari – da Zamfara da Sokoto na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu amfani da babura tare da kashe ɗaruruwan mutane.
Mazauna Katsina sun gudanar da wata zanga-zangar nuna ɓacin ransu game da yadda gwamnati ta gaza kare rayukansu.bbchausa na wallafa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com




