Labarai

An Gano Dan Minista Pantami Da Aka Sace A Bauchi

An Gano dan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami, da aka yi zargin cewa an sace shi, a garin Dambam, daya daga cikin Kananan Hukumomin Jihar Bauchi.
Daya daga cikin malaman yaron ta shaida wa wakilinmu cewa, “Mun fito ne daga gidansu, ya dawo gida yanzu an same shi a Dambam wadanda suka sace shi suka ajiye shi a shingen binciken jami’an tsaro, daga nan ne aka dawo da shi gida.
Da daddare aka sanar da mu cewa an sace shi, amma mun gode Allah Madaukakin Sarki wadanda suka sace shi suka yar da shi,”
Babban Limamin Masallacin Jum’a na Minista Pantamin da ke Bauchi, Imam Hussaini ya tabbatar da cewa yaron yanzu haka yana gida.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai rahoton lamarin ga rundunarsu ba.
Ya ce, “Mun tuntubi dukkan jami’an ’yan sandan da ke Bauchi suka ce ba a kai rahoton lamarin ba, ko da ya faru ba mu sani ba.
“Abin da muke bukata daga jama’a shi ne su taimaka mana da sahihan bayanai game da masu aikata laifi a tsakanin alu’mma don daukar matakin da ya dace, kuma idan akwai wata matsala suyi maza su kai rahoto ga ’yan sanda.”
A ranar Alhamis ne a dandalin sada zumunta aka yi ta yayata cewa anyi garkuwa da dan Ministan a kusa da ginin NIDB da ke Bauchi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button