Labarai

Amurka Ta Ayyana Wasu ‘Yan Najeriya Shida A Matsayin Masu Taimakawa Boko Haram

Wannan mataki da aka dauka a yau, ya biyo bayan hukunci da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yankewa wadannan mutane da ke tallafawa ayyukan ta’addanci.” Sanarwar ta ce.
Voahausa ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta fitar da sunayen wasu ‘yan Najeriya shida wadanda ta ayyana su a matsayin masu taimakawa kungiyar Boko Haram da kudade da wasu ayyuka.
Sashen da ke kula da kadarorin ketare a Hukumar Baitul Malin Amurka ne ya fitar da sunayen, kamar yadda Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.
Mutanen sun hada da, Abdurrahman Ado Musa, Salihu Yusuf Adamu, Bashir Ali Yusuf, Muhammed Ibrahim Isa, Ibrahim Ali Alhassan, da kuma Surajo Abubakar Muhammad.

Amurka Ta Ayyana Wasu ‘Yan Najeriya Shida A Matsayin Masu Taimakawa Boko Haram
Amurka Ta Ayyana Wasu ‘Yan Najeriya Shida A Matsayin Masu Taimakawa Boko Haram

Sanarwar ta nuna cewa, mutanen suna kuma taimakawa kungiyar ta hanyoyin da dama da suka hada yi musu hidindimu da samar da tallafi a fannin fasahohi na zamani.
A cewar sanarwar, yanzu haka sunayan mutanen ya shiga wani kundi na wadanda suke tallafawa ayyukan ta’addanci, kamar yadda umarnin shugaban kasa na 13224 ya ba da izini kan wadanda suke tallafawa kungiyar.
“Wannan mataki da aka dauka a yau, ya biyo bayan hukunci da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yankewa wadannan mutane da ke tallafawa ayyukan ta’addanci.” Sanarwar ta ce.
A ranar 14 ga watan Nuwambar 2013, Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ayyana Boko Haram a matsayin ta ‘yan ta’adda.
Boko Haram ce ke da alhakin dumbin hare-haren da ake kai wa a arewa da arewa maso gabashin Najeriya da kuma wasu yankunan Tafkin Chadi da ke Kamaru, Chadi, da Nijar, wadanda suka halaka dubban mutane tun daga 2009.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button