Jaruman Kannywood 6 wanda suka rasu aka kasa maye gurbin su
Kamar irin su Marigayi Rabilu Musa Ibro wanda ya zama lamba ta daya sannan kuma babban jigo a finafinan Barkwanci.
To hakama acikin shekara ta 2021 Masana’antar ta Kannywood ta kara yin wani babban rashin na wasu Fitattun Jaruman nata, wanda suka hada Tsohuwar jaruma.
Fitaccen mai daukar hoto da kuma mawaki, wanda wannan rashi ya matukar tada hankalin jaruman da Masana’antar baki daya.
Marigayiya Hajiya Fatima tarauni wacce akafi sani da Kaka ta bawa acikin shiri mai dogon zango na Dadin kowa wanda gidan talabijin ta Arewa24 take RND gabatarwa.
Allah yayi wannan jaruma rasuwa a jahar kano ran Alhamis 11 ga watan 3 na shekara ta 2021, an kumayi janaizarta a garin na kano kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Dumbin jaruman Kannywood da kuma tashar arewa24 sun nuna alhinin su da addua ga marigayiyar na wannan babban rashi nata da akayi Muna fatan Allah yaji kanta ya mata rahama ameen.
Hajia zainab musa booth tsohuwar jarumar Kannywood wacce mahaifiyace ga maryam booth, Ramadan booth da kuma Amude booth.
Allah yayiwa jarumar rasuwa ne ran 2 ga watan 7 na shekara ta 2021, bayan rashin lafia da tasha fama da ita.
kamar yadda jaruma maryam booth wacce diyace ga marigayiyar ta wallafa labarin rasuwar mahaifiyar tata a shafin nata na instagram.
Anyi janaizarta Kamar yadda addinin musulunci ya tanadar muna fatan Allah yaji kanta ya haskaka kabarinta ameen.