An shiga jimami: Jama’a sun shiga tashin hankali da zub da hawaye yayin da amarya ta rasu ana daf da aurenta


Wata kyakkyawar amarya ta amsa kiran mahaliccinta a lokacin da ake shirye shiryen aurenta.
Amarya mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce ake kira da Ummi da angonta ASP Abdulmuhyi Bagel Garba a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, amma sai rai yayi halinsa.
Shafin mr_mrs_arewa ne ya wallafa labarin mutuwar amaryar a Instagram tare da hoto da katin gayyatar auren nasu.
View this post on Instagram
Shafin ya rubuta:
“Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun
“Feb 5th
“Dan Allah ku karbi wannan a matsayin jan hankali don yiwa Ummi addu’a. “Allahumma gafirlaha warhamha waafiha wa’afu’anha” Allah ya yafe mata kura-kuranta sannan ya bata jannah.”
Labarin mutuwarta ya taba zukatan mutane da dama a shafin soshiyal midiya inda suka ta kwararo mata addu’a cike da nauyin zuciya.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin sharhin mutanen a kasa:
minalbash_collections ta ce:
“Allahu ya jikanta da rahama yasa aljanna ce makomarta amin”
anchuchi ta rubuta:
“Allah ya jikan ta da rahma “
zainab_biu ta yi martani:
“Allahu Akbar Aure jiya ta innalillahi wa inailaihi raju,u”
fatima_aliyi_ibrahim ta ce:
“Allah yamata rahama❤️❤️❤️”
Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja
twinzcollections2 ta rubuta:
“ALLAH YA jikanki Ummina”
habibatisamohammed ta rubuta:
“Inna Lillahi wa’ina Ilaihi raji’un. Allah Ya Jikan ta da rahama Ya bada hakuri”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






We are appreciating your efforts.