AddiniLabarai

Hotuna: Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannunsa

Advertisment

Masha Allah labari mai daɗi da majiyarmu ta leadership hausa na ruwaito wani hazaƙin dalibi da Allah ya albarkaci shigowarsa addinin musulunci yayi wata bajinta a duniyar Musulunci.

‘Yan watanni bayan ya karbi Addinin Musulunci wani matashi mai sunan Ibrahim ya rubuta Al-kur’ani mai girma da rubutun hannu a garin Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Malaminsu Abu Anas Al-baahy ya ce, bayan ya shiga ajinsu na ‘Faslu Imamu Malik Bin Anas’ sai ya tarar da shi da Al-kur’aninsa a gefe yana ta kokarin ganin ya rubuta Al-kur’ani ta hanyar kwafa yana rubuta shi a littafi.

Malamin na su ya bayyana cewa, hakika ganin haka ya sanya shi tsaya wa cak cike da farin ciki yana kallon ikon Allah.

Advertisment

Shi dai wannan matashin da sunansa Ibrahim, sunan mahaifinsa Sylvester, watanni biyar baya ko harafin Alifun baya iya furtawa balantana ya rubuta, cikin ikon Allah bayan shigarsa Islamiyyar At-tatbiqul Islamiya, yau ga shi AlQur’anin ma yake kokarin ya rubuce wa duka.Hotuna: Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannunsa Hotuna: Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannunsa Hotuna: Yan Watanni Bayan Shigarsa Musulunci Ya Rubuta Al-Qur’ani Da Hannunsa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button