Saboda So da kaunar Buhari wani ya sanyawa jaririnsa suna Buhari


Malam Maiwada ‘Danmallam, ya bada labarin wani mutumi da ya samu haihuwa, ya kuma yi wa shugaban Najeriya takwara da wannan jaririn.
Maiwada ‘Danmallam ya bayyana wannan ne a shafinsa na Facebook a yau, Litinin 17 ga watan Junairu, 2021, inda mutane ke ta faman yi wa jaririn addu’o’i.
Legit na ruwaito Kamar yadda ya fada, Danmallam yace wani abokinsa ne ya turo masa sako cewa matarsa ta haihu a ranar Larabar da ta wuce, ya sa wa yaro suna Buhari.
A cewar wannan mutumi da ya samu kyakkyawan yaro, kauna da soyayyar Mai girma shugaban kasa ta sa ya zabi wannan suna watau Muhammadu Buhari.
“Ina kwana mai girma jagorana. Ubangiji ya azurta ni da iyalina da samun jariri namiji a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022.”
“Kuma saboda irin kaunar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na sa wa jaririn sunansa, Muhammadu Buhari.”
“Da mahaifiyar da yaron duk su na lafiya.” – Mai jego.
Me jama’a suke fada?
- Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a game da wannan karuwa da aka samu. Yayin da wasu suke yi wa iyalin barka, wasu kuma akasin hakan su ke yi.
Allah Ya raya Muhammadu Buhari, Ya albarkaci rayuwarsa – Jafar Jafar
Ina fatan ba za su canza ra’ayi, su canzawa yaron suna daga baya kamar yadda wasu suka yi ba. – Yamai Mohammed
Muhammadu babban suna… Allah Ya raya shi cikin musulunci, Yayi masa albarka. Amin
Muhammad Azare
Masha Allah – Sham Faliya Sharon
Allahumma Aameen. Wasu za su ji haushin wannan abin, babu gaira babu dalili. Sai su yi ta bakin ciki! – Yusuf Muhammad Illo
Amin – SK Usman
Alhamdu lillah Allah yasa masa albarka ya rayashi rayuwar musulunci Allah yasa ya gaji halayen mai sunan gaskiya da rik’on amana.Allah ya kareshi daga sharrin zamani da na shedan a gaida mai jego muna taya ta murna da fatan alheri – Abdulrahman Masanawa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





Kai barakallah da samun nasara na haihuwar mai sunan wanda ake fadinsa akasa samun wani sai shi a kasarmu nigeria shine kalmar kamar haka: NIGERIA SAI MAI GASKIYA Sai ace ansan da wanda ake sabida gaskiyar tayi kama dashi