Labarai

Mata Musulmai sune suka fi kowanne mata tsafta da tsarki a duniya – Bincike

Matar da mijinta ya sake ta sai ta tsaya tayi zaman jira na akalla watanni uku, haka ma wacce mijinta ya mutu sai tayi zaman takaba na tsawon watanni hudu kafin su sake yin wani auren
Idan ya zama tana da ciki, za ta sake jira har sai lokacin da ta haifi jaririn. Wannan koyarwa da Musulmai suke bi ta bawa masanan kimiyya na wannan zamani matukar mamaki.
A jikin kowanne namiji akwai wani ruwa da yake dauke da sinadarin abinci na proteins, kuma na kowanne namiji ya bambanta dana kowa.
Idan mace ta auri wani namiji bayan rabuwarta da tsohon mijinta, kuma ta bari ya kwanta da ita ba tare da tayi idda ba, kamar kutse ne da wasu suke yi a na’ura mai kwakwalwa.
An tabbatar a kimiyyance cewa wannan zaman idda da takaba da mata suke yi bayan sun rabu da mazajensu, yana cire wannan ruwan na tsohon mijinsu daga jikinsu a lokacin da suke al’ada a tsakanin wadannan watanni.
Hakan ya sanya Allah A’aza wa Jal ya ce watanni hudu, wannan lokaci da aka diba saboda a cire ruwan wancan daya mijin ne.
Wannan ne ya sanya masana a fannin lafiya suka gabatar da wani bincike akan wasu mata Musulmai ‘yan Afrika da suke zaune a kasar Amurka. Sun gano cewa duka matan sune dauke da iya ruwan mijinsu ne kawai.
Masanan sun sake gabatar da binciken a jikin wasu mata wadanda ba Musulmai ba, inda suka tarar da ruwan mutane da yawa a jikinsu, wasu maza biyu wasu kuma uku.
Tun daga wannan ranar masanan suka bayyana cewa matan Musulmai sune suka fi tsafta da tsarki a fadin duniya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button