Labarai

[Bidiyo] Babu wanda ya Dadatsa Jikin Hanifa – Cewar Abdulmalik Tanko

Advertisment

Shugaban Makarantar Noble Kids dake unguwar yan Kaba kwanar Dakata, a birnin Kano, Abdulmalik Mohammed Tanko, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ba gaskiya ba ne rahotannin da ake yayatawa cewa, sun yi gunduwa-gunduwa da jikin Hanifa Abdullahi bayan ta mutu kafin suka binne ta.
Abdulmalik wanda ake zargi da garkuwa da kuma kashe Hanifa, ya bayyana cewa, an sa Hanifa a cikin buhu ne wanda ba shi da girma sosai da ya zama dole kafarta ta tankware. Ya ce da yake ita karamar yarinya ce kuma buhun yana da fadi sai aka dan tankwara kafarta yadda dukan jikinta zai shiga buhun amma babu wanda ya dauki wuka ya illata jikinta.
Bisa ga cewarshi, tankware kafafunta kafin sa ta buhun da aka binne ta a ciki, ya sa lokacin da aka tono ta, aka ga kamar an karya gababuwanta, amma a Zahiri ba wanda ya daddatsa ta ko wani abu makamancin haka.
Ya kuma bayyana cewa, an cire rigar sanyi da baje, da kuma hijabin Hanifa ne daga jikinta bayan ta mutu, aka rika aikawa iyayenta a matsayin shaida domin neman kudin fansa. Dangane da lokacin, da kuma wurin da Hanifa ta rasu, Abdulmalik ya ce, ta kwana biyar a gidanshi tare da iyalinshi kafin ya fitar da ita zuwa wani wuri inda ta kwana daya, kafin ta cika ranar goma ga watan Disamba, watau kwana shida bayan yin garkuwa da ita
Ga bidiyo nan ku saurara.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button