Labarai

Wasu sun ba hamata iska a gaban Ka’aba

Auzubillahi wannan abu dami yayi kama kaje Ibadah a dakin Allah amma har ta sanya ka fada da dan uwanka musulmi wannan abu sam baiyi ba.

Ga wani rahoto da jaridar Bbchausa na wallafa akan yadda anka baiwa hamata iska a bakin dakin ka’aba da ke kasar Saudiya.

Jami’an tsaro na musamman da ke kula da aikin Hajji da Umrah a Saudiyya sun ƙaddamar da bincike kan faɗa da ya ɓarke tsakanin wasu mutane biyu a yankin Al-Mas’a da ke cikin Masallacin Harami na Makkah a ranar Alhamis.

Ba a samu rahoton wani rauni ba sakamakon faɗan da suka yi amma an ɗauki matakai game da mutanen biyu, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Jami’an tsaron da ke aikin kula da Hajji da Umrah sun yi kira ga masu ibadah da su mutunta alfarmar Ka’aba da kuma kiyayewa tare da kasancewa cikin natsuwa yayin gudanar da aikin ibadar umrah da sauran ibadu a Masallatai biyu masu alfarma a Saudiyya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button