Hamisu breaker Mawakin Farko da ya shiga Sahun mawakan Nigeria a YouTube 2021
Fitaccen mawakin Hausa Hamisu Breaker ya shiga jerin mawakan Najeriya da suka ci kasuwa a dandalin Youtube a shekarar 2021 mai karewa.
Dandalin Turntable Charts mai fitar da kididdigar wakokin da aka fi saurare da kallo a shafin na Youtube ne ya fitar da alkaluman.
Voahausa ta ruwaito Cikin jerin mawakan Najeriya da suka hada da mafi akasari na kudu, mawakin na Jaruma ya shiga sahun mawaka nag aba-gaba da aka fi jin wakokinsu.
Alkaluman sun nuna mawakin a saman mawakan kudu irinsu Joe Boy, Patoranking, Yemi Alade, Tekno, Kizz Daniel da sauransu.
View this post on Instagram
Mawaki Davido ne a saman teburin sai Omah Lay a matsayi na biyu sai Wizkid a matsayi na uku.
Tuni dai Breaker, wanda shi ne mawaki daya tilo daga Arewacin Najeriya da ya samu shiga sahun gaba ya wallafa wadannan alkaluma a shafinsa na Instagram.
“Alhamdulillah 2021.” Breaker ya rubuta a kasan alkaluman.