An soke lasisin wasu kamfanonin shirya finafinai biyu a jihar Kano – Abba El-Mustapha


Kamfanonin da hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta soke lasisin kamfanin shirya finafinai su ne na Amart Entertainment da na Kannywood Enterprise Limited mallakin Aisha Amart bisa zargin tura waƙoƙi da finafinai ba bisa doka ba.
Kamar yadda shugaban hukumar tace fina finai a jihar kano abba El-Mustapha ya shedawa manema labari a wani zantawa da yayi da freedom radio kano sunka zanta da shi yana mai cewa.
“To wannan mata yanzu duk mun soke lasisin ta da take taƙama da shi na gidan kamfamin fina finan ta da kuma kamfanin kasuwancin ta na dallanci fina finai gaba daya mun soke, kuma laifin da tayi yana gaba kotu zata zo ta girbi abinda ta shukka ita hajiya A’isha amart.
Akwai kamfanuka guda biyu da take amfani da su na farko shine na raraba kaya shine kannywood enterprises limited Sa’a nan kuma akwai na shirya fina finai Amart entertainment , dukkansu mun soke lasisin su da suke wannan gida yanzu babu ita babu wannan gida.- inji Abba El-Mustapha
Yanzu masu yin downloading idan taje kamasu ya yakamata suyi?
“Zasu kai rahoto a kusa da hukumar yan sanda take a kusa da su, ku duk inda sunka san akwai jami’an tsaro, ku sukai rahoto zuwa ma’aikatarmu , ku kuma kungiyar su, ta tsaya tsayin daka wajen ganin an dawo musu da hakkin su, ita kuma wannan ƙungiya zata tsaya wajen ganin an dawo musu da hakkin su, su masu downloading.”
Abba El-Mustapha yace zasu cigaba da kare martaba duk masu tura wakoki ko fina finai da ke jihar kano.
“Su cigaba da bin doka idan har zasu bi doka su zauna lafiya su saye abin da sunka san ba malakar su bane malakar masu shiryawa ne wadanda sunka zo sunka kawo musu,musamman waɗannan masu rarabawa,domin sai sun saya ne masana’ata zata cigaba du fita daga daukar kayan da bana su ba suna sayarwa.
Su sani wannan kwamiti da munka nada ya kamasu to rikicin ya koma gaban alkali domin su gani ba irin wannan rikici bane na fina finai bane, yan fastocin ne kawai su tabbatar da sun saya saboda yan kuɗin ƙalilan ne , mu kuma zamu cigaba da kare musu hakkin su, a duk lokacin da ake kokarin a tozarta su ko kuma a chi musu mutunci suma subi doka”.-inji shugaba abba elmustapha.
Abba elmustapha ya bukaci wanda bai da rigista yakamata yaje yayi rigista.