Labarai

Ya kamata namiji yayi jima’i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike

Ya kamata  namiji yayi jima'i akalla sau 21 a wata, Sabon Bincike
Masana sun yi alhinin yawaitar cutar dajin mafitsara cikin mazaje masu shekaru 40 da abinda yayi sama
Bincike na gudana kan yadda za’a magance wannan cutar cikin mazaje masu yawan shekaru
Binciken Jami’ar Harvard ya alakanta yawan yin jima’i da raguwar kamuwa da cutar
Wani sabon bincike ya nuna cewa ya kamata kowani namiji yayi inzali akalla sau 21 a wata domin kariya daga cutar dajin mafitsara da ke yawaita cikin maza.
A cewar masu bincike a Jami’ar Harvard dake Amurka, an gudanar da wannan bincike ne kan maza 31,925.
Binciken wanda aka wallafa a mujallar Ilimi ta European Urology, mazaje 31,925 sun bayyana adadin lokutan da suke inzali a wata.
Daga wannan bincike, masanan sun gano cewa yawan inzali na rage yiwuwar kamuwa da cutar dajin mafitsara da kashi uku.
“Mun yi bincike kan shin yawan inzali lokacin da mutum ke girma na da alaka da kamuwa da cutar daji cikin mazaje a Amurka.”
“Mun gano cewa akwai raguwar yiwuwar kamuwa da cutar ‘Kansa’ cikin mazajen da suka fada mana suna inzali sosai lokacin da suke girma fiye da wadanda ba suyi sosai.”
Source: legit

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button