Miliyoyin Mutane sun Halarci Maulidin Sheikh Dahiru Bauchi Daren Jiya (bidiyo da hotuna)
Taron Maulidin Manzon Allah SAW wanda ake gudanarwa a karkashin jagorancin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA, ya samu halartan manyan baki daga sassan daban -daban na kasar mu Najeriya da kasashen waje kamar Senegal, Chad, Camaroun, Niger da sauran su.
Maulana Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana soyayyan Manzon Allah SAW a matsayin wajibi ga al’umma duk wani matsayin da dan’adam ya samu ya samu ne saboda Manzon Allah SAW ya zama wajibi ga kowanne mutum ya kaunaci Annabi a kowanne hali. Ya godewa mahalarta wannan taro wanda aka saba gabatar duk shekara.
A nasa jawabin gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Muhammadu (Kauran Bauchi) ya godewa jama’a wanda suka zo daga nesa dama cikin garin Bauchi tare da fatan Allah ya maida kowa gida lafiya.
Taron ya samu halartan manyan baki daga sassan kasar nan dama duniya, an gabatar da addu’o’i daga Sheikh Dahiru Bauchi.
Ga bidiyon nan
https://youtu.be/r_g89nyMM4U
Allah ya maimaita mana, Allah ya maida kowa gida lafiya, ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiin




Daga: Tijjaniyya Media News