Addini
SANARWA: An Ga Watan Ramadan A Nijeriya – Sarkin Musulmi Sa’a d Abubakar Na ukku
Advertisment
SANARWA SANARWA
Mai Alfarma sarkin musulmi Sa’ad Abubakar Na Ukku cewa Mun samu Labarin cewa anga Jinjin watan Ramadan a sassan Nigeria daga Shuwagabannin kwamitin ganin wata.
Wanda mai Alfarma yana cewa A gobe Juma’a 24/4/2020 shine Daya ga watan Ramadan.
Alfarma ya kara da cewa gobe Kowa ya tashi da azumi.
Advertisment
Mai alfarma sarkin Musulmi ya kara da cewa mutane su zama masu addu’ar zaman lafiya da kuma wannan cutar Covid 19 Allah ya yaye mana ita.
Mai alfarma sarkin Musulmi yayi kira ga masu hannu da shunni da su taimakawa marasa karfi.
Wanda a karshe yayi fatan Allah yasa ayi azumi lafiya a kare lafiya.
Allah yasa amshi ibadodinmu baki daya amen.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com