Addini

Zamu Hada Kai Da Izala Matukar Idan Ta Daina Abubuwa Guda Uku ~ Sheikh Dahiru Bauchi

Zamu Hada Kai Da Izala Matukar Idan Ta Daina Abubuwa Guda Uku ~Sheikh Dahiru BauchiWata sabuwa inji yan chacha anya wannan abubuwan da babban shehi ya kawo kungiyar izalatu bidi’ah wa’ikamatus sunnah zasuyi na’am da shi kuwa domin kuwa suna yakar bidi’a da nuna girman waliyai da Alkur’ani ya fadi da hadisan manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
To shine a yau majiyarmu Hausaloaded munka samu rahoto daga shafin fityanulmedia sunka wallafa akan abun da shehin su yace na hadin kansu da izala.

Idan Dan Izala Ya Daina Abubuwa Uku To Shi Kenan Zamu Hada Kai Dasu, Daman Sune Suka Tafi Suka Barmu Suka Ce Mu Ba Musulmai Bane, Suke Kafirta Musulmi Amma Mu(Dariqa) Bamu Da Abokin Gaba Kullum Kofarmu a Bude Take Don Hadin Kai Idan Har Suka Dawo Suka Daina Yin Wadannan Miyagun Laifukan:

*1. Kafirta Musulmi.
*2. Kafirta Dariku.
*3. Sannan Suka Daina Kafirta Waliyyai.

Shi Kenan Hadin Kai Ya Zo Amma Muddin Basu Daina Ba, Muna Nan Kamar Kullum Bamu Canja Ba”

….Inji SHAYKH TAHIRU USMAN BAUCHI.”

Shin kuna ganin kungiyar izalatu bidi’ah wa’ikamatus sunnah zasu karbi wannan abubuwan domin hadin kai?.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. A gani wannan abu ne me saukin gaske. Farko dai Shehi yai mana bayani, meye banbancin: 1. Kafirta Musulmi da 2. Kafirta Dariqu? Shin ya fitar da Dariqu ne daga cikin jinsin Musulmi? To a ina suka faada kenan? Jinsin Kiristawa ko Yahudawa ko kuma ina?
    To sannan sai a chi gaba da fayyacewa. Sai ya kawo misalin kalaman yan izala da suka tabbatar da cewa eye lallai suna aikata dukkanin wayannan “laifuka” guda uku. A “laifi” me lamba ta uku ana bukatar ya kawo sunan waliyyin da izala ta kafurta. To bayan an gama wannan tattaunawar ne, chikin ilimi da ladabi da natsuwa, ba tare da hayaniya ko hauragiya ba, sai mu gani shin akwai bukatar wani bangare ya tubar ma wani koko babu. Haza Wasalam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button