El-Rufa’i ya haramta sana’ar Achaba don yaki da ƴan bindiga a Kaduna


Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Samuel Aruwan, inda sanarwar ta ce masu Keke Napep za su rika aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na dare.
Dcl sun ruwaito cewa sanarwar ta kuma ce, gwamnatin jihar ta sanya dokar cewa duk masu motocin haya su yi musu fenti launin dorowa da baki nan da kwanaki 30.
Samuel Aruwan ya ce an kuma hana sana’ar bumburutu wato sayar da fetur a cikin jarkoki da galaluwa a kananan hukumomin Kajuru, Chikun, Kachia, Kagarko Birnin Gwari da Giwa.
Sanarwar ta ce ana nan ana shirye-shiryen katse layukan sadarwa a wasu sassan jihar.



