Da dumi-dumi: Atiku Ya karawa Dukkan Ma’aikatansa Albashi Mafi Karanci N33,000
Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yiwa dukkan ma’aikatan da ke karkashinsa karin albashi zuwa N33,000.
Mohammed El-Yakub, Direktan Gotel Communications, kamfanin sadarwa mallakar Atiku da ke Yola ya tabbatarwa Sahara Reporters a yau Alhamis inda ya ce, “za a fara biyan sabuwar albashin mafi karanci na N33,000 daga watan Nuwamban 2018. Kuma karin albashin ya shafi dukkan wadanda ke aiki karkashin Atiku har da masu hidima a gidajensa.”
El-Yakub ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin mutane 100,000 da ke karbar albashi a kowanne wata a karkashin tsohon mataimakin shugaban kasar.
Atiku ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya amince da N30,000 a matsayin albashi mafi karanci kamar yadda kwamitin albashi da shugaban kasar ya kafa suka shawarci shi a cikin rahoton da suka gabatar masa.