Duk Duniya Babu Namijin da na ke so da kauna kamar Abdul’aziz Ganduje in ji Aseeyah Abdullahi
Hausawa kance kowa da kidan da ya karbesa ita wannan kuma babu wanda take so tamkar dan gwaggo wanda a kwanan baya anka ce yakai karar mama gwaggo EFCC akan almundahana akan bidiyon dala. Sai gashi kwatsam mun samu wani rubutu daga wani marubuci a facebook mai suna janaidu amadu doro da cewa ita aseeyah abdullahi ta kamu da son Abdulaziz Abdulaziz ganduje.
“Shahararriyar matashiyar budurwar nan da ta yi kaurin suna a kafar sadarwar Facebook wajen rubuce-rubucen barkwanci Aseeyah Abdullahi ta bayyana cewa duk Duniya babu namijin da ta ke tsananin so kamar dan gwamnan jihar Kano Abdul’aziz Ganduje tun bayan da ta yi Arba da hoton matashin ta kamu da matsanancin sonshi a ruhinta.
Budurwar ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook inda ta yi rubutu kamar haka :
“Idan na 6oye abinda ke cikin zuciyata na cuci kaina kuma hakan zai iya zama mun ciwo Ni fa tunda na ga hoton bawan Allah nan na ji nan duniya babu namijin da na ke so kamarshi.
A cewar budurwar Don Allah a ce ma mama gwaggo da Baba ganduje ina gaishe da su”.
Shin ko ku na ganin Burin matashiyar zai cika kuwa ?”