Yanzu – Yanzu : Gwamna Tambuwal Ya Jagoranci Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Harkat Tsaro A Jahar Sokoto
A yau laraba 18 ga watan agusta, maigirma gwamnan jihar sokoto Rt Hon Aminu waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) ya kira taron masu ruwa da tsaki a jihar sokoto a kowane bangaren al’umma domin tattauna matsalolin tsaro dake addabar wasu sassa na jihar sokoto.

Taron wanda ya kunshi maigirma mataimakin gwamna Hon Dr Muhammad Manir Dan Iya (Walin Sokoto) tsofaffin gwamnoni, Attahiru Dalhatu Bafarawa da kuma Senator Aliyu Magatakarda Wamakko, shuwagabannin hukumomin tsaro dake a wannnan jiha, shuwagabannin al’umma na siyasa, sarakuna, malamai duk suna a wurin qarqashin jagorancin maigirma gwamna Tambuwal.
Taron wanda ya gudana a babban dakin taro na kasa da kasa dake a Kasarawa, anan cikin birnin sokoto.


Dafatar Allah SWT yasa anyi wannna taron cikin nasara ya kuma kaddari atattauna abinda zai kawo zaman lafiya da kanciyar hankali ga al’ummar jihar sokoto da kasa baki daya don darajar Alkur’ani Maigirma.
Bilya Yariman Barebarin Fcbk
S.A to Governor Tambuwal
Laraba 18th August, 2021

