Kannywood

Shin Da Gaske Hadiza Muh’d Tace Ba zata sake Aure Ba sai Lahira?

A yan kwanakinnan labarai sun cika kafofin yada labarai, wanda a ke danganta shi da cewar, Fitacciyar jaruma Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadizan Saima, ta yi wani furuci da ta ke cewa, ita ta hakura da aure, don haka ita da aure sun yi sallama, sai dai a lahira.
To sai dai wannan labarin bai yi wa jaruma Hadiza Muhammad dadi ba, domin kuwa ta ce ita Sam babu wani dan jarida da suka yi hira da shi, har ta fadi wannan kalmar.
Hadiza Muhammad ta bayyana hakan ne a lokacin da ta Kira wakilin jaridar Dimukaradiyya, domin ta bayyana halin da ta samu kan ta a dai-dai lokacin da ta ji ana yada wannan labarin.

Hadiza saima Muhammad

Inda ta ke cewa “Abin ya ba ni mamaki kuma ya ba ni takaici, kamar ni ina Musulma na tashi a cikin Muslunci, sannan na ce na hakura da aure. Ai duk wata mace tagari kai har ma wacce ba tagari ba, tana fatan ta mutu a dakin mijin ta ne. To bare ni da na yi aure har na haifi yara biyu, na san dadin auren, wai kuma ni ce zan fadi wannan maganar, gaskiya ba haka ba ne, babu wata Jarida da muka yi hira da ita na fadi hakan. ”
Ta ci gaba da cewar “Ka dube ni ba tsohuwa ba ce ni, da har zan ce shekaru na sun kai na hakura da aure, don haka babu ma yadda za a yi wannan maganar ta fita daga baki na, ina ganin wasu ne dai su ke fadar hakan don su kashe mini kasuwa. To in Allah ya yarda sai sun ji kunya, don za su ga na samu miji na yi aure, don haka maganar su ba za ta Hana ni yin aure ba, ina fatan Allah ya kawo mun miji nagari, da zan yi aure na yadda zan kare rayuwa ta a gidan mijina” inji ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button