Labarai

Engr Abba kabir Yusuf ( Abba Gida Gida ya koma Jam’iyyar NNPP

A hukumance Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koma jami’iyyar (NNPP

Tsohon dan takarar gwamnan Kano a jami’iyyar PDP a zaben 2019 Abba Kabiru Yusuf ya sanar da komawa sabuwar jami’iyyar NNPPP daga jami’iyyarsa ta PDP.
Freedom radio ta ruwaito wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a ranar Lahadi mazabarsa ta Diso dake karamar hukumar Gwale a nan Kano.
Hadimi namu samman ga Abba Kabiru Yusuf ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi.
Cikin wadanda suka halarci taron sauya shekar Abba Gida-Gida sun hada da mataimakinsa Kwamrade Aminu Abdussalam da kuma shugaban jami’iyyar ta NNPP a nan Kano Haruna Umar Dogowa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button