Kisan Musulmi a jos- Idan ku ka ga kwana 2 banyi fostin ba to komai na iya faruwa….
Shahararen jarumin Kannywood Bello Muhammad Bello, ya bayyana cewa idan aka ga kwana biyu bai wallafa komai a shafinsa ba, to komai na iya faruwa, inda yake nuna bacin ransa kan kisan kiyashin da aka yi wa Musulmai a garin sa na Jos.
Jarumin wanda yake da tsananin nuna kishin addini da ta da jijiyar wwuya a duk sanda aka taba Allah da ma’aikinsa, haka kuma a duk sanda wani abu makamancin haka ya faru jarumin yana fitowa a zahirri ya nuna alhininsa akan wannan lamari.
A wannan karon ma jarumin ya nuna bacin ransa matuka, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta cewa:
Ko a dauki mataki kan kafiran Jos kan abinda suka yiwa Musulmai matafiya ko mu dauki doka a hannunmu.
Jarumin bai tsaya a nan ba ya kuma sake rubutu a kasan wannan, inda ya ce:
Ba wani boye-boye! Baza a doke ka a hanaka kuka ba.
Masu posting idan zakuyi posting ku fito ku saki zance kawai ku daina boye-boye don tsoron kafirai ko wadanda suke daurewa kafirai gindi a Kasarnan.
Arnan Plateau Tsinannu Ne!
Idan kuka ga kwana biyu banyi posting ba, to komai ma na iya faruwa don na quna ban tsoron wuta.”
Ko kuna da abin cewa ?